- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 605–538 BC
The Babylonian Exile
Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Makoki 3:7kusan 588 K.H.
Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.
- Makoki 3:8kusan 588 K.H.
Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata.
- Makoki 3:9kusan 588 K.H.
Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace.
- Makoki 3:10kusan 588 K.H.
Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye,
- Makoki 3:11kusan 588 K.H.
ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako.
- Makoki 3:12kusan 588 K.H.
Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa.
- Makoki 3:13kusan 588 K.H.
Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa.
- Makoki 3:14kusan 588 K.H.
Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.
- Makoki 3:15kusan 588 K.H.
Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci.
- Makoki 3:16kusan 588 K.H.
Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura.
- Makoki 3:17kusan 588 K.H.
An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.
- Makoki 3:18kusan 588 K.H.
Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
- Makoki 3:19kusan 588 K.H.
Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai.
- Makoki 3:20kusan 588 K.H.
Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.
- Makoki 3:21kusan 588 K.H.
Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba.
- Makoki 3:22kusan 588 K.H.
Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
- Makoki 3:23kusan 588 K.H.
Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne.
- Makoki 3:24kusan 588 K.H.
Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.”
- Makoki 3:25kusan 588 K.H.
Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;
- Makoki 3:26kusan 588 K.H.
yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.
- Makoki 3:27kusan 588 K.H.
Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro.
- Makoki 3:28kusan 588 K.H.
Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi.
- Makoki 3:29kusan 588 K.H.
Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege.
- Makoki 3:30kusan 588 K.H.
Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci.
- Makoki 3:31kusan 588 K.H.
Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada.