Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings

580 ayoyi · 175 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yehowash sarkin Isra’ila ya kama Amaziya sarkin Yahuda, ɗan Yowash, ɗan Ahaziya a Bet-Shemesh. Sa’an nan Yehowash ya kawo shi Urushalima ya farfasa katangar Urushalima daga Ƙofar Efraim har zuwa Ƙofar Kusurwa, wani sashe mai tsawon ƙafa ɗari shida.

  2. Ya kwashe dukan zinariya da azurfa da dukan kayayyakin da aka samu a haikalin Allah waɗanda suke a ƙarƙashin kulawar Obed-Edom, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.

  3. Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya rayu shekara goma sha biyar bayan mutuwar Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila.

  4. Game da sauran ayyukan mulkin Amaziya, daga farko zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.

  5. Sa’ad da Amaziya ya bar bin Ubangiji, aka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma suka aiki mutane suka bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.

  6. Aka dawo da shi a kan doki, aka binne shi tare da kakanninsa a Birnin Yahuda.

  7. Sai dukan mutanen Yahuda suka ɗauki Uzziya wanda yake da shekara goma sha shida da haihuwa, suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa Amaziya.

  8. Shi ne wanda ya sāke gina Elot ya kuma mai da shi ga Yahuda bayan Amaziya ya huta tare da kakanninsa.

  9. Uzziya yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya ce; ita daga Urushalima ce.

  10. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda mahaifinsa Amaziya ya yi.

  11. Ya nemi Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya koyar da shi a tsoron Allah. Muddin ya nemi Ubangiji, Allah ya ba shi nasara.

  12. Ya yi yaƙi da Filistiyawa ya kuma rushe katangar Gat, Yabne da kuma Ashdod. Sa’an nan ya sāke gina garuruwa kusa da Ashdod da sauran wurare a cikin Filistiyawa.

  13. Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa da kuma a kan Larabawa waɗanda suke zama a Gur-Ba’al da kuma a kan Meyunawa.

  14. Ammonawa suka kawo haraji wa Uzziya, sunan da ya yi kuwa ya bazu har iyakar Masar, domin ya zama mai iko sosai.

  15. Uzziya ya gina hasumiyoyi a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, a Ƙofar Kwari da kuma a kusurwar katanga, ya kuma yi musu katanga.

  16. Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma.

  17. Uzziya ya kasance da gogaggun mayaƙa, a shirye su fito ɓangarori-ɓangarori bisa ga yawansu yadda Yehiyel magatakarda, da Ma’asehiya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin fadawa.

  18. Yawan shugabannin iyali a bisa jarumawa sun kai 2,600.

  19. A ƙarƙashin shugabancinsu akwai mayaƙa 307,500 horarru don yaƙi, mayaƙa masu ƙarfi don su taimaki sarki a kan abokan gābansa.

  20. Uzziya ya tanada garkuwoyi, māsu, hulunan kwano, kayan sulke, baka da majajjawa don mayaƙan gaba ɗaya.

  21. A Urushalima ya yi na’urori da gwanaye suka sarrafa don amfani a hasumiyoyi da kuma a kusurwar kāriya don harbin kibiyoyi da jefan manyan duwatsu. Sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako sosai har ya zama mai iko.

  22. Amma bayan Uzziya ya zama mai iko, sai ɗaga kai ya kai shi ga fāɗuwa. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa ba, ya kuma shiga haikalin Ubangiji don yă ƙone turare a bagaden turare.

  23. Azariya firist tare da waɗansu firistoci tamanin na Ubangiji masu ƙarfin hali suka bi shi ciki.

  24. Suka kalubalance shi suka ce, “Ba daidai ba ne, Uzziya, ka ƙone turare ga Ubangiji. Wannan aikin firistoci zuriyar Haruna ne, waɗanda aka tsarkake don ƙone turare. Ka bar wuri mai tsarki, gama ka kasance marar aminci; kuma Ubangiji Allah ba zai girmama ka ba.”

  25. Uzziya wanda yake da farantin wuta a hannunsa a shirye don ƙone turare, ya husata. Yayinda yake fushi da firistocin a gabansu a gaban bagaden turare a haikalin Ubangiji, sai kuturta ta faso a goshinsa.