Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem

271 ayoyi · 117 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Yoshuwa ya karkashe waɗannan sarakuna guda biyar, ya kuma rataye kowannensu a bisa itace inda jikunansu suka kasance har yamma.

  2. A Hebron ya yi mulki a bisa Yahuda shekara bakwai da wata shida, a Urushalima kuma ya yi mulki a bisa Isra’ila da Yahuda shekara talatin da uku.

  3. Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.”

  4. Duk da haka, Dawuda ya kame kagarar Sihiyona, wadda ta zama Birnin Dawuda.

  5. A ranar, Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kame Yebusiyawa, dole yă yi amfani da wuriyar ruwa don yă kai ga waɗannan ‘guragu da makafi’ waɗanda suke abokan gāban Dawuda.” Shi ya sa suka ce, “ ‘Makafi da guragu’ ba za su shiga fadan sarki ba.”

  6. Sai Dawuda ya zauna a kagarar, ya kuma kira ta Birnin Dawuda. Ya gina wuraren da suke kewaye da ita, tun daga madogaran gini zuwa ciki.

  7. To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, “Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah.” Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki.

  8. Sa’ad da waɗanda suke ɗaukan akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai yă yi hadayar bijimi da saniya mai ƙiba.

  9. Dawuda, sanye da efod lilin, ya yi ta rawa a gaban Ubangiji da dukan ƙarfinsa,

  10. yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni.

  11. Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal ’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.

  12. Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, aka ajiye shi a inda aka shirya masa a cikin tentin da Dawuda ya shirya dominsa. Dawuda kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama a gaban Ubangiji.

  13. Bayan ya gama yin hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki.

  14. Sa’an nan ya rarraba abinci, da ƙosai, dabino, da waina ga kowane mutum a cikin dukan jama’ar Isra’ila, maza da mata. Dukan mutane kuwa suka watse zuwa gidajensu.

  15. Da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima, don yă hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake wahal da mutane, “Ya isa, ka janye hannunka.” A lokacin kuwa Mala’ikan Ubangiji yana tsaye a masussukar Arauna, mutumin Yebus.

  16. Da Dawuda ya ga mala’ikan da ya bubbugi mutane, sai ya ce wa Ubangiji, “Ni ne na yi zunubi, na kuma yi abin da ba daidai ba. Waɗannan tumaki ne kawai. Me suka yi? Bari hukuncinka yă sauko a kaina da iyalina.”

  17. A ranar, Gad ya koma wurin Dawuda ya ce, “Ka tashi, ka tafi ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna, mutumin Yebus.”

  18. Saboda haka Dawuda ya haura, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Gad.

  19. Da Arauna ya hangi Dawuda da mutanensa suna zuwa wajensa, sai ya fita a guje, ya je ya rusuna a gaban sarki.

  20. Arauna ya ce, “Me ya sa ranka yă daɗe, sarki ya zo wajen bawansa?” Dawuda ya ce, “Don in saya masussukarka, saboda in gina wa Ubangiji bagade don a tsayar da annoban da suke a bisa mutane.”

  21. Arauna ya ce wa Dawuda, “Bari ranka yă daɗe, sarki yă ɗauki duk abin da ya ga dama yă miƙa shi. Ga shanu, don hadaya ta ƙonawa, ga kuma kayan masussuka da itacen shanu, don itace.”

  22. Dukan wannan, ranka yă daɗe, Arauna ya ba wa sarki. Arauna ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahnka yă karɓa.”

  23. Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.” Sai Dawuda ya saya, ya kuma biya masussukar, da shanun a bakin shekel hamsin na azurfa.

  24. Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban.

  25. Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji.