- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz.
Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ’ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.
Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.”
Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya,
Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su.
Saurara! Zan sa masa wani ruhun da zai sa yă ji wata jita-jitar da za tă sa yă koma ƙasarsa. A can zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”
Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna.
To, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana zuwa masa da yaƙi. Saboda haka ya sāke aika manzanni zuwa wurin Hezekiya cewa,
“Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’
Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka?
Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar?
Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?”
Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji.
Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya.
Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka ji; ka buɗe idanunka ya Ubangiji ka gani; ka saurari kalmomin da Sennakerib ya aiko don yă yi wa Allah mai rai ba’a.
“Da gaske ne, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriya sun hallakar da waɗannan al’ummai da ƙasashensu.
Sun jefar da allolinsu cikin wuta, suka hallaka su, gama ba alloli ba ne, katakai ne da kuma duwatsu, ayyukan hannuwan mutane.
To, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, don dukan mulkokin duniya su san cewa kai kaɗai, ya Ubangiji ne Allah.”
Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya.
Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi, “ ‘Budurwar Sihiyona ta rena ka tana kuma yin maka ba’a. Diyar Urushalima ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.
Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo? Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka, har ka tā da idanunka da fahariya? Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila!
Ta wurin manzanninka ka tara wa Ubangiji zagi. Ka kuma ce, “Da yawa kekunan yaƙina na haye kan ƙwanƙolin duwatsu, wurin mafi tsawo na Lebanon. Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo mafi daraja na itacen fir nasa. Na ratsa har can tsakiyar kurmi, mafi kyau na kurminsa.
Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.”
“ ‘Ba ka taɓa ji ba? Tun da daɗewa na ƙaddara haka. Tuntuni kuwa na shirya shi; yanzu kuma na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu katanga tarin duwatsu.
Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye, suka razana aka kuma kunyata su. Suna kama da tsirai a gona, kamar sabon toho kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.