Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem

271 ayoyi · 117 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Dukan waɗanda suke zaune a Majalisar suka kafa wa Istifanus ido, suka kuma ga fuskarsa ta yi kama da ta mala’ika.

  2. Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.

  3. Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.

  4. Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.

  5. Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi.

  6. To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai.

  7. Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.

  8. Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.

  9. Kwana uku bayan isowa a lardin, sai Festus ya haura daga Kaisariya zuwa Urushalima,

  10. inda manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka bayyana a gabansa suka kuma gabatar da ƙararsu a kan Bulus.

  11. Suka roƙi Festus a gaggauce a matsayin alfarma gare su, da yă sa a mai da Bulus Urushalima, gama sun ’yan kwanto su kashe shi a hanya.

  12. Festus ya amsa ya ce, “Bulus yana tsare a Kaisariya, ni da kaina kuma zan je can ba da daɗewa ba.

  13. Ku sa waɗansu daga cikin shugabanninku su tafi tare da ni su kawo ƙararsu a kan mutumin a can, in ya aikata wani laifi.”

  14. Bayan ya yi kwanaki takwas ko goma tare da su, sai ya gangara zuwa Kaisariya, kashegari kuma ya kira a yi zaman kotu ya kuma umarta a kawo Bulus a gabansa.

  15. Da Bulus ya bayyana, sai Yahudawan da suka gangaro daga Urushalima suka tsaya kewaye shi, suna kawo ƙarar masu tsanani da yawa a kansa, waɗanda ba su iya tabbatarwa ba.

  16. Sa’an nan Bulus ya kāre kansa ya ce, “Ban aikata wani laifi game da dokokin Yahudawa ko game da haikali ko kuma game da Kaisar ba.”

  17. Festus, da yake yana so yă yi wa Yahudawa alfarma, sai ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a gabana a kan waɗannan zarge?”

  18. Bulus ya amsa ya ce, “Yanzu ina tsaye a gaban kotun Kaisar, inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wani laifi ga Yahudawa ba, kai da kanka ma ka san da haka sarai.

  19. In kuwa ina da wani laifin da ya isa kisa, ban ƙi in mutu ba. Amma in ƙarar da waɗannan Yahudawa suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda yake da iko ya ba da ni a gare su. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!”

  20. Bayan Festus ya yi shawara da majalisarsa sai ya ce, “Ka ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar. To, ga Kaisar kuwa za ka tafi!”

  21. Bayan ’yan kwanaki sai Sarki Agiriffa da Bernis suka iso Kaisariya don su yi wa Festus gaisuwar bangirma.