Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem: Disciples persecuted and dispersed from

7 ayoyi · 117 fannoni

Ayoyi game da Disciples persecuted and dispersed from

  1. Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.

  2. Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.

  3. Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.

  4. Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi.

  5. To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai.

  6. Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.

  7. Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.