Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem: Miraculous gift of the Holy Spirit first given at
Ayoyi game da Miraculous gift of the Holy Spirit first given at
Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.
Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.
Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.
Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.
To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.