Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem: Signs preceding its destruction

15 ayoyi · 117 fannoni

Ayoyi game da Signs preceding its destruction

  1. Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.

  2. Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.

  3. Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.

  4. “Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.

  5. A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,

  6. annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.

  7. Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,

  8. amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

  9. Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.

  10. “Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),

  11. Suka tambaye shi suka ce, “Malam, yaushe waɗannan za su faru? Kuma wace alama za tă nuna cewa suna dab da faruwa?”

  12. Ya amsa ya ce, “Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su.

  13. Sa’ad da kuka ji labarin yaƙe-yaƙe, da juye juyen mulki, kada ku tsorota. Dole ne waɗannan abubuwa su fara faruwa, amma ƙarshen ba zai zo nan da nan ba.”

  14. Sai ya ce musu, “Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki zai tasar wa mulki.

  15. Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.