Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem: Conquest of Mount Zion in, made by David
Ayoyi game da Conquest of Mount Zion in, made by David
Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin
suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda.
Dawuda ya ce, “Duk wanda ya jagoranci yaƙi a kan Yebusiyawa zai zama babban shugaban mayaƙa.” Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba.