- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa,
sai ’yan’uwan Yesu suka ce masa, “Ya kamata ka bar nan ka tafi Yahudiya, don almajiranka su ga ayyukan banmamaki da kake yi.
Ba wanda yake so a san shi da zai yi abu a ɓoye. Da yake kana yin waɗannan abubuwa, sai ka nuna kanka ga duniya.”
Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.
Saboda haka Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna; amma a gare ku kowane lokaci daidai ne.
Duniya ba za tă iya ƙinku ba, amma ni take ƙi domin ina shaida cewa ayyukanta mugaye ne.
Ku ku tafi Bikin, ba zan haura zuwa wannan Bikin ba yanzu, domin lokacina bai yi ba tukuna.”
Da ya faɗa haka, sai ya dakata a Galili.
Amma fa, bayan ’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye.
A Bikin kuwa, Yahudawa suka yi ta nemansa, suna cewa, “Ina mutumin yake?”
A cikin taron kuwa aka yi ta raɗe-raɗe game da shi. Waɗansu suka ce, “Shi mutumin kirki ne.” Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ai, ruɗin mutane yake.”
Amma ba wanda ya ce kome a fili game da shi don tsoron Yahudawa.
Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa.
Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.
Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.
Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.
Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.
To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.
To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane.
Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus,
amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba.
Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”
Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa.
Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka.
Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.”