Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem

271 ayoyi · 117 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta; su wawaye ne, gama ba su san hanyar Ubangiji ba, ko abubuwan da Allahnsu yake bukata ba.

  2. Saboda haka zan tafi wurin shugabanni in yi musu magana; tabbatacce sun san hanyar Ubangiji, da abubuwan da Allahnsu yake bukata.” Amma da nufi guda su ma suka karye karkiyar suka tsintsinke sarƙoƙin.

  3. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima.

  4. Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi.

  5. Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima.

  6. A shekara ta tara ta Zedekiya sarkin Yahuda, a wata na goma, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fita yaƙi da Urushalima da dukan sojojinsa ya kuma yi mata ƙawanya.

  7. A rana ta tara ga watan huɗu a shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya, sai aka huda katanga.

  8. Sa’an nan dukan fadawan sarkin Babilon suka shiga suka zazzauna a Ƙofar Tsakiya. Wato, Nergal-Sharezer na Samgar-Nebo, Sarsekim wani babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da dukan sauran fadawan sarkin Babilon.

  9. Sa’ad da Zedekiya sarkin Yahuda da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu; suka bar birnin da dare ta hanyar lambun sarki, ta ƙofar da take tsakanin katanga biyu, suka nufi waje Araba.

  10. Amma sojojin Babiloniyawa suka bi su, suka ci wa Zedekiya a filayen Yeriko. Suka kama shi suka kai shi wurin Nebukadnezzar a Ribla a ƙasar Hamat, inda aka yanke masa hukunci.

  11. A can Ribla sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idanunsa aka kuma kashe dukan manyan mutanen Yahuda.

  12. Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya ya kuma buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babilon.

  13. Sai Babiloniyawa suka cinna wa fadar da kuma gidajen mutane wuta suka farfasa katangar Urushalima.

  14. “Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Urushalima ce wannan, wadda na kafa a tsakiyar al’ummai, da ƙasashe kewaye da ita a ko’ina.

  15. Duk da haka cikin muguntarta ta yi tayarwa a kan dokokina da ƙa’idodina fiye da al’ummai da ƙasashe kewaye da ita. Ta ƙi dokokina ba tă kuwa bi ƙa’idodina ba.

  16. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce kin yi ƙin ji fiye da al’umman da suke kewaye da ke ba ki kuma bi ƙa’idodina ko ki kiyaye dokokina ba. Ba ki ma dace da matsayin al’umman da suke kewaye da ke ba.

  17. “Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce Ni kaina ina gāba da ke, Urushalima, kuma zan hukunta ki a gaban al’ummai.

  18. Sa’an nan ya kawo ni mashigin filin. Na duba, na kuma ga rami a bango.

  19. Ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka haƙa cikin bangon.” Da na haƙa cikin bangon sai na ga ƙofar shiga a can.

  20. Sai ya ce mini, “Shiga ka ga mugaye da kuma abubuwa banƙyamar da suke yi a can.”

  21. Na kuwa shiga na duba, sai na ga zāne-zāne ko’ina a bangon na kowane irin abubuwa masu rarrafe da kuma dabbobi masu ƙazanta da dukan gumakan gidan Isra’ila.

  22. za a ba wa ƙofofin birnin sunaye kabilan Isra’ila. Ƙofofi uku a gefen arewa za su zama ƙofar Ruben, ƙofar Yahuda da ƙofar Lawi.

  23. A gefen gabas, wanda yake da tsawon kamu 4,500 zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Yusuf, ƙofar Benyamin da ƙofar Dan.

  24. A gefen kudu, wanda yake da tsawon kamu 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Simeyon, ƙofar Issakar da ƙofar Zebulun.

  25. A gefen yamma, wanda yake da tsawon kamun 4,500, zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Gad, ƙofar Asher da kuma ƙofar Naftali.