Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jerusalem

271 ayoyi · 117 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Amma na san wurin zamanka da fitarka da shigarka da yadda kake fushi da ni.

  2. Domin kana fushi da ni reninka ya iso kunnuwata, zan sa ƙugiyata a hancinka da linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma a ta hanyar da ka zo.’

  3. “Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya, “Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa, baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara. Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe, ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa.

  4. Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da ’ya’ya a bisa.

  5. Gama daga Urushalima za a sami ragowa, daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.

  6. “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga birnin nan ba ko yă harba kibiya a nan. Ba zai kusace ta da garkuwa ko yă yi mata zoben yaƙi ba.

  7. Ta hanyar da ya zo ne zai koma; ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji.

  8. Zan kāre birnin nan in cece ta, saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”

  9. A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina.

  10. Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.

  11. Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.

  12. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, zan jawo wa Urushalima da kuma Yahuda masifar da duk kunnen da ya ji, sai ya kusa suma.

  13. Zan auna Urushalima da ma’aunin da na yi amfani da shi a kan Samariya, zan kuma yi amfani da magwajin da na yi amfani da shi a kan gidan Ahab. Zan shafe Urushalima yadda mutum yake wanke kwano yă kife.

  14. Zan rabu da ragowar gādona, in kuma miƙa su ga maƙiyansu. Abokan gābansu za su washe suka kuma kwashi ganima daga gare su,

  15. domin sun aikata mugunta a idanuna, suka kuma tsokane ni tun daga ranar da kakanninsu suka fito daga Masar, har yă zuwa yau.”

  16. Fir’auna Neko ya sa shi a sarƙa a Ribla a ƙasar Hamat don kada yă yi mulki a Urushalima, sa’an nan ya sa wa Yahuda harajin talenti ɗari na azurfa, da talenti ɗaya na zinariya.

  17. Fir’auna Neko ya naɗa Eliyakim ɗan Yosiya sarki a maimakon mahaifinsa, ya kuma canja masa suna zuwa Yehohiyakim. Ya ɗauki Yehoyahaz ya kai Masar, a can ya mutu.

  18. Yehohiyakim ya riƙa biyan Fir’auna Neko azurfa da zinariyar da ya umarta. Don yă yi haka sai ya riƙa karɓar azurfa da zinariya daga mutanen ƙasar, kowa bisa ga ƙarfinsa.

  19. A rana ta goma ga wata na goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya ne Nebukadnezzar sarkin Babilon tare da dukan rundunan yaƙinsa, ya tasam wa Urushalima. Ya yi sansani a bayan birnin, ya kewaye ta da shirin yaƙi.

  20. Haka birnin ta kasance a kewaye har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.

  21. A rana ta tara ta watan huɗu, lokacin da yunwa ta yi tsanani a birnin, babu kuma abinci domin mutane su ci.

  22. Sai aka huda katanga sa’an nan dukan sojoji suka tsere da dare a ƙofa tsakanin katanga biyu da suke kusa da lambun sarki, ko da yake Babiloniyawa sun kewaye birnin. Suka tsere suka nufi Araba.

  23. Amma sojojin Babiloniyawa suka bi sarki, suka cin masa a filayen Yeriko. Dukan sojojinsa kuwa suka rabu da shi suka watse.

  24. Aka kama shi, aka kai shi gaban sarkin Babilon a Ribla, inda aka yanke masa hukunci.

  25. Suka kashe ’ya’yan Zedekiya a gabansa, sa’an nan aka ƙwaƙule idanunsa. Suka daure shi da sarƙar tagulla, suka kai shi Babilon.