Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yohanna 14:2kusan 33 M.

    A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri.

  2. Yohanna 14:3kusan 33 M.

    In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake.

  3. Yohanna 14:4kusan 33 M.

    Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”

  4. Yohanna 14:5kusan 33 M.

    Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”

  5. Yohanna 14:6kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.

  6. Yohanna 14:7kusan 33 M.

    Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.”

  7. Yohanna 14:8kusan 33 M.

    Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.”

  8. Yohanna 14:9kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’?

  9. Yohanna 14:10kusan 33 M.

    Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa.

  10. Yohanna 14:11kusan 33 M.

    Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu.

  11. Yohanna 14:12kusan 33 M.

    Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba.

  12. Yohanna 14:13kusan 33 M.

    Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban.

  13. Yohanna 14:14kusan 33 M.

    Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.

  14. Yohanna 14:15kusan 33 M.

    “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.

  15. Yohanna 14:16kusan 33 M.

    Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada,

  16. Yohanna 14:17kusan 33 M.

    Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.

  17. Yohanna 14:18kusan 33 M.

    Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.

  18. Yohanna 14:19kusan 33 M.

    Ba da daɗewa ba, duniya ba za tă ƙara ganina ba, amma za ku gan ni. Don ina raye, ku ma za ku rayu.

  19. Yohanna 14:20kusan 33 M.

    A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku.

  20. Yohanna 14:21kusan 33 M.

    Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”

  21. Yohanna 14:22kusan 33 M.

    Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?”

  22. Yohanna 14:23kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi.

  23. Yohanna 14:24kusan 33 M.

    Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.

  24. Yohanna 14:25kusan 33 M.

    “Duk wannan na faɗa ne yayinda ina tare da ku.

  25. Yohanna 14:26kusan 33 M.

    Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.