Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yohanna 12:40kusan 33 M.

    “Ya makantar da idanunsu ya kuma taurare zukatansu, don kada su gani da idanunsu, ko su fahimta a zukatansu, ko kuwa su juyo, har in warkar da su.”

  2. Yohanna 12:41kusan 33 M.

    Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa.

  3. Yohanna 12:42kusan 33 M.

    Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi. Amma saboda Farisiyawa ba su furta bangaskiyarsu ba, don tsoron kada a kore su daga majami’a;

  4. Yohanna 12:43kusan 33 M.

    gama sun fi son yabon mutane, fiye da yabon Allah.

  5. Yohanna 12:44kusan 33 M.

    Sa’an nan Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Duk wanda ya gaskata da ni, ba ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.

  6. Yohanna 12:45kusan 33 M.

    Duk mai dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne.

  7. Yohanna 12:46kusan 33 M.

    Na zo cikin duniya a kan ni haske ne, don duk wanda ya gaskata da ni, kada yă zauna a cikin duhu.

  8. Yohanna 12:47kusan 33 M.

    “Duk mai jin kalmomina bai kuwa kiyaye su ba, ba ni ba ne nake shari’anta shi. Gama ban zo domin in yi wa duniya shari’a ba, sai dai domin in cece ta.

  9. Yohanna 12:48kusan 33 M.

    Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe.

  10. Yohanna 12:49kusan 33 M.

    Gama ba don kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ne ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa da kuma yadda zan faɗe shi.

  11. Yohanna 12:50kusan 33 M.

    Na san cewa umarninsa yana kai ga rai madawwami. Saboda haka duk abin da na faɗa na faɗe shi ne kamar dai yadda Uba ya ce in faɗa.”

  12. Yohanna 13:1kusan 33 M.

    Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.

  13. Yohanna 13:2kusan 33 M.

    Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu.

  14. Yohanna 13:3kusan 33 M.

    Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah;

  15. Yohanna 13:4kusan 33 M.

    saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa.

  16. Yohanna 13:5kusan 33 M.

    Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura.

  17. Yohanna 13:6kusan 33 M.

    Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, “Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?”

  18. Yohanna 13:7kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane.”

  19. Yohanna 13:8kusan 33 M.

    Sai Bitrus ya ce, “Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Yesu ya amsa ya ce, “Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni.”

  20. Yohanna 13:9kusan 33 M.

    Sai Siman Bitrus ya ce, “To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!”

  21. Yohanna 13:10kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata yă wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba.”

  22. Yohanna 13:11kusan 33 M.

    Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, “Ba kowa ba ne yake da tsabta.”

  23. Yohanna 13:12kusan 33 M.

    Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, “Kun fahimci abin da na yi muku?

  24. Yohanna 13:13kusan 33 M.

    Kuna ce da ni ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ daidai ne kuwa, gama haka nake.

  25. Yohanna 13:14kusan 33 M.

    Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna.