Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Yohanna 13:15kusan 33 M.

    Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku.

  2. Yohanna 13:16kusan 33 M.

    Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi.

  3. Yohanna 13:17kusan 33 M.

    Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su.

  4. Yohanna 13:18kusan 33 M.

    “Ba dukanku nake nufi ba; na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa don a cika Nassi ne da ya ce, ‘Wanda ya ci burodina tare da ni ya tasar mini.’

  5. Yohanna 13:19kusan 33 M.

    “Ina faɗa muku yanzu tun kafin yă faru, domin in ya faru, ku gaskata cewa ni ne Shi.

  6. Yohanna 13:20kusan 33 M.

    Gaskiya nake gaya muku, ‘Duk wanda ya karɓi wani da na aiko, ni ne ya karɓa ke nan. Kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.’ ”

  7. Yohanna 13:21kusan 33 M.

    Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

  8. Yohanna 13:22kusan 33 M.

    Almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake.

  9. Yohanna 13:23kusan 33 M.

    Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi.

  10. Yohanna 13:24kusan 33 M.

    Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?”

  11. Yohanna 13:25kusan 33 M.

    Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?”

  12. Yohanna 13:26kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman.

  13. Yohanna 13:27kusan 33 M.

    Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.”

  14. Yohanna 13:28kusan 33 M.

    Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.

  15. Yohanna 13:29kusan 33 M.

    Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu.

  16. Yohanna 13:30kusan 33 M.

    Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. A lokacin kuwa dare ya yi.

  17. Yohanna 13:31kusan 33 M.

    Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa.

  18. Yohanna 13:32kusan 33 M.

    In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikin Ɗan, Allah kuwa zai ɗaukaka Ɗan zuwa ga zatinsa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.

  19. Yohanna 13:33kusan 33 M.

    “’Ya’yana, zan kasance da ku na ɗan ƙanƙani lokaci ne. Za ku neme ni. Kuma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, haka nake gaya muku yanzu. Inda zan tafi, ba za ku iya zuwa ba.

  20. Yohanna 13:34kusan 33 M.

    “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna.

  21. Yohanna 13:35kusan 33 M.

    Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”

  22. Yohanna 13:36kusan 33 M.

    Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”

  23. Yohanna 13:37kusan 33 M.

    Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.”

  24. Yohanna 13:38kusan 33 M.

    Sai Yesu ya amsa ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku!

  25. Yohanna 14:1kusan 33 M.

    “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.