- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Fitowa 36:7kusan 1491 K.H.
Saboda abin da suke da shi ya fi abin da ake bukata domin aikin.
- Fitowa 36:8kusan 1491 K.H.
Dukan maza masu fasaha a cikin sauran masu aikin suka yi tabanakul da labule goma na tuƙaƙƙun lallausan lilin na shuɗi, da shunayya, da jan zare, aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.
- Fitowa 36:9kusan 1491 K.H.
Tsawon kowane labule, kamu ashirin da takwas ne, fāɗinsa kuma kamu huɗu. Dukan labulen, girmansu ɗaya ne.
- Fitowa 36:10kusan 1491 K.H.
Suka ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, suka kuma yi haka da sauran labule biyar ɗin.
- Fitowa 36:11kusan 1491 K.H.
Suka yi rami a gefe-gefen labulen da zaren ruwan bula, haka kuma suka yi da ɗayan gefen na biyu ɗin.
- Fitowa 36:12kusan 1491 K.H.
Suka kakkafa rammuka hamsin a daidai bakin labulen, haka kuma suka yi a kan labule na biyun. Haka aka ɗaɗɗaura rammukan nan da junansu yă zama kamar abu guda.
- Fitowa 36:13kusan 1491 K.H.
Sa’an nan suka yi maɗaurai hamsin na zinariya, suka yi amfani da su don daurin kashi biyu na labulen saboda tabanakul yă zama ɗaya.
- Fitowa 36:14kusan 1491 K.H.
Suka yi labule da gashi akuya goma sha ɗaya don tenti a bisa tabanakul.
- Fitowa 36:15kusan 1491 K.H.
Dukan labule goma sha ɗayan girmansu ɗaya ne, tsawonsa kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne.
- Fitowa 36:16kusan 1491 K.H.
Suka harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, suka kuma harhaɗa shida wuri ɗaya.
- Fitowa 36:17kusan 1491 K.H.
Sa’an nan suka yi rammuka hamsin a gefen labule na kashe na farko, haka kuma a gefen labule na ƙarshen na kashi biyar.
- Fitowa 36:18kusan 1491 K.H.
Suka yi maɗaurin tagulla hamsin don su ɗaura tenti yă zama ɗaya.
- Fitowa 36:19kusan 1491 K.H.
Sai suka yi wa tentin murfi da fatun rago da aka rina ja, a bisa wannan kuwa akwai murfin fatun shanun teku.
- Fitowa 36:20kusan 1491 K.H.
Suka yi katakan tabanakul da itacen ƙirya.
- Fitowa 36:21kusan 1491 K.H.
Tsawon kowane katako kamu goma ne, kaurinsa kuma kamu ɗaya da rabi,
- Fitowa 36:22kusan 1491 K.H.
tare da katakai a fiƙe ɗaura da juna. Haka suka yi da dukan katakan tabanakul.
- Fitowa 36:23kusan 1491 K.H.
Suka yi katakai ashirin don gefen kudu na tabanakul
- Fitowa 36:24kusan 1491 K.H.
suka kuma yi rammukan azurfa arba’in don katakan su shiga ƙarƙashinsu, rammuka biyu domin kowane katako, ɗaya ƙarƙashin kowanne da aka fiƙe.
- Fitowa 36:25kusan 1491 K.H.
A ɗaya gefen, gefen arewa na tabanakul, suka yi katakai ashirin
- Fitowa 36:26kusan 1491 K.H.
da rammuka arba’in na azurfa, biyu-biyu don kowane katako.
- Fitowa 36:27kusan 1491 K.H.
Suka yi katako shida don iyaka ta ƙarshe, wato, gefen yamma na tabanakul,
- Fitowa 36:28kusan 1491 K.H.
aka kuma yi katakai biyu domin kusurwoyi tabanakul a iyaka ta ƙarshe.
- Fitowa 36:29kusan 1491 K.H.
A waɗannan kusurwoyi biyu, an ninka katakan sau biyu daga ƙasa har sama, aka kuma sa su cikin zobe guda; dukansu biyu an yi su daidai.
- Fitowa 36:30kusan 1491 K.H.
Ta haka aka sami katakai takwas da rammukan azurfa goma sha shida, biyu-biyu a ƙarƙashin kowane katako.
- Fitowa 36:31kusan 1491 K.H.
Suka kuma yi sanduna na itace ƙirya, biyar domin katakan da suke a gefe guda na tabanakul,