Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 36:32kusan 1491 K.H.

    biyar domin waɗanda suke ɗayan gefen da kuma biyar domin katakan da suke gefen yamma na iyaka ta ƙarshen tabanakul.

  2. Fitowa 36:33kusan 1491 K.H.

    Suka sa sandan da yake a tsakiya yă wuce daga wannan gefe zuwa wancan.

  3. Fitowa 36:34kusan 1491 K.H.

    Sai suka dalaye katakan da zinariya, suka yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Suka kuma dalaye sandunan da zinariya.

  4. Fitowa 36:35kusan 1491 K.H.

    Suka kuma yi labule da shuɗi, shunayya, jan zare, da kuma lallausan lilin, suka kuma yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.

  5. Fitowa 36:36kusan 1491 K.H.

    Suka yi dogayen sanduna huɗu na itacen ƙirya dominsa, suka dalaye su da zinariya. Suka yi ƙugiya na zinariya dominsa, suka yi rammuka huɗu da azurfa.

  6. Fitowa 36:37kusan 1491 K.H.

    Suka yi wa ƙofar tenti labulen shuɗi, shunayya, jan zare, da kuma lallausan lilin, aikin gwaninta;

  7. Fitowa 36:38kusan 1491 K.H.

    suka kuma yi dogayen sanduna biyar da ƙugiya dominsu. Suka dalaye saman dogayen sandunan da abin daurinsu da zinariya, suka kuma yi rammukansu guda biyar da tagulla.

  8. Fitowa 37:1kusan 1491 K.H.

    Bezalel ya yi akwatin alkawari da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi.

  9. Fitowa 37:2kusan 1491 K.H.

    Ya dalaye shi da zinariya zalla, ciki da waje, ya kuma yi zubin zinariya kewaye da shi.

  10. Fitowa 37:3kusan 1491 K.H.

    Ya yi masa zubi huɗu na zoban zinariya, ya kuma ɗaura su a ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a wannan gefe da kuma biyu a wancan.

  11. Fitowa 37:4kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ya yi sanduna na itacen ƙirya, ya dalaye shi da zinariya.

  12. Fitowa 37:5kusan 1491 K.H.

    Sai ya sa sandunan a cikin rammukan da suke gefen Akwatin don ɗaukarsa.

  13. Fitowa 37:6kusan 1491 K.H.

    Ya yi murfin jinƙai da zinariya zalla, wato, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi.

  14. Fitowa 37:7kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ya yi kerubobi biyu da ƙeraren zinariya a ƙarshen murfin jinƙan.

  15. Fitowa 37:8kusan 1491 K.H.

    Ya yi kerub a iyakar gefe ɗaya, ya yi ɗayan kuma a wancan gefe; a iyakan nan biyu, ya yi su a haɗe da murfin.

  16. Fitowa 37:9kusan 1491 K.H.

    Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwatar da murfin da fikafikansu. Kerubobin suna fuskantar juna, suna kuma kallon murfin.

  17. Fitowa 37:10kusan 1491 K.H.

    Suka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa ƙafa ɗaya, tsayinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi.

  18. Fitowa 37:11kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan suka dalaye shi da zinariya zalla, suka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi.

  19. Fitowa 37:12kusan 1491 K.H.

    Suka kuma yi masa baki mai fāɗin tafi hannu, suka yi zubin zinariya a bisa bakin.

  20. Fitowa 37:13kusan 1491 K.H.

    Suka yi zubin zobai huɗu na zinariya don tebur ɗin, sai suka ɗaura su a kusurwoyi huɗu inda ƙafafu huɗun suke.

  21. Fitowa 37:14kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan aka sa zoban kurkusa da bakin don riƙe sandunan da ake amfani da su wurin ɗaukan teburin.

  22. Fitowa 37:15kusan 1491 K.H.

    An yi sandunan da ake ɗaukan tebur da itacen ƙirya, aka kuma dalaye su da zinariya.

  23. Fitowa 37:16kusan 1491 K.H.

    Suka kuma yi duk kayayyakin teburin da zinariya zalla, farantansa, kwanonin tuya, kwanoninsa, da kuma butoci domin hadaya ta sha.

  24. Fitowa 37:17kusan 1491 K.H.

    Suka yi wurin ajiye fitila da zinariya zalla, suka yi gindinsa da kuma gorar jikinsa, da ƙerarriyar zinariya. Kwaf wurin ajiye fitila da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da wurin ajiye fitilan.

  25. Fitowa 37:18kusan 1491 K.H.

    Akwai rassa guda shida da suka miƙe daga gefe wurin ajiyar fitilar, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.