Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The High Priest

142 ayoyi · 65 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ka shirya ƙyallen da za a manna a ƙirji don neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa efod ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.

  2. Zai zama murabba’i, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kuma kamu ɗaya, a naɗe shi biyu.

  3. Sa’an nan ka yi jeri huɗu na duwatsu masu daraja a kansa. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.

  4. A jeri na biyu, a sa turkuwoyis, da saffaya, da emeral.

  5. A jeri na uku, a sa yakin, da idon mage da ametis.

  6. A jeri na huɗu, a sa kirisolit, da onis, da yasfa. Ka sa su a tsaiko na zinariya.

  7. A bisa duwatsun nan goma sha biyu, sai a zāna sunayen ’ya’yan Isra’ila bisa ga kabilansu goma sha biyu. Za a zāna sunayen kamar hatimi.

  8. “Ka yi wa ƙyallen maƙalawa a ƙirjin tuƙaƙƙun sarƙoƙin zinariya zalla.

  9. Ka yi zobe biyu na zinariya saboda ƙyallen maƙalawa a ƙirjin, ka kuma ɗaura su a kusurwoyin ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  10. Ka ɗaura sarƙoƙin zinariyan nan biyu a zoban a kusurwan ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  11. Ka kuma sa sauran bakunan sarƙoƙin nan biyu a kan tsaikon nan biyu, kana haɗa su da ƙyallen kafaɗa na efod a gaba.

  12. Ka yi zobai biyu na zinariya ka ɗaura su ga sauran kusurwoyi ƙyallen maƙalawa a ƙirji, a gefen ciki kusa da efod.

  13. Ka ƙara zobai biyu, ka kuma ɗaura su a bakin ƙyallen da ya sauka daga kafaɗa ta gaban efod, kusa da mahaɗin ƙyallaye biyu a bisa ɗamara na efod.

  14. Za a ɗaura zoban ƙyallen maƙalawa a ƙirji a zoban efod da shuɗiyar igiya, domin ƙyallen maƙalawa a ƙirji yă zauna a bisa abin ɗamarar efod, don kada yă kunce.

  15. “Duk sa’ad da Haruna zai shiga Wuri Mai Tsarki, zai shiga riƙe da sunayen ’ya’yan Isra’ila a zuciyarsa a kan ƙyallen maƙalawa a ƙirji na neman nufin Allah, domin yă zama abin tunawa a gaban Ubangiji.

  16. “Ka yi taguwar efod da shuɗi duka,

  17. ka yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A kuma naɗe wuyan rigar yă yi kauri domin kada yă yage.

  18. Za a yi wa bakin rigar ado da fasalin ’ya’yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu.

  19. Za ka jera su bi da bi, wato, ’ya’yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya kewaye da bakin rigar.

  20. Dole Haruna yă sa shi sa’ad da yake hidima. Za a ji ƙarar ƙararrawar sa’ad da zai shiga Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji, da sa’ad da ya fita, don kada yă mutu.

  21. “Ka yi allo na zinariya zalla, ka kuma yi rubutu a kansa kamar na hatimi, haka, Mai tsarki ga Ubangiji.

  22. Ka ɗaura shi da igiyar ruwa bula domin a haɗa shi da rawani; zai kasance a gaban rawanin.

  23. Zai kasance a goshin Haruna, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa baye-bayensu masu tsarki. Zai kasance a goshin Haruna kullayaumin, domin su zama abin karɓa ga Ubangiji.

  24. Ubangiji ya yi magana da Musa bayan mutuwar ’ya’yan Haruna biyu maza waɗanda suka mutu sa’ad da suka kusaci Ubangiji.

  25. Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna, kada yă riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule koyaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada yă mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.