Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The High Priest: Robe of the ephod

5 ayoyi · 65 fannoni

Ayoyi game da Robe of the ephod

  1. “Ka yi taguwar efod da shuɗi duka,

  2. ka yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A kuma naɗe wuyan rigar yă yi kauri domin kada yă yage.

  3. Za a yi wa bakin rigar ado da fasalin ’ya’yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu.

  4. Za ka jera su bi da bi, wato, ’ya’yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya kewaye da bakin rigar.

  5. Dole Haruna yă sa shi sa’ad da yake hidima. Za a ji ƙarar ƙararrawar sa’ad da zai shiga Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji, da sa’ad da ya fita, don kada yă mutu.