Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The High Priest

142 ayoyi · 65 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bulus ya amsa ya ce, “’Yan’uwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa, ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’”

  2. Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai.

  3. Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali.

  4. Shi ya sa dole yă miƙa hadayu domin zunubansa, da kuma domin zunuban mutane.

  5. Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna.

  6. Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma.

  7. Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade.

  8. Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba.

  9. Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana.

  10. Ya zama firist ne ba saboda ya cika wata ƙa’ida ta zama zuriyar Lawi ba, sai dai bisa ga ikon ran da ba a iya hallakawa.

  11. Gama nassi ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”

  12. Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. Waɗansu sun zama firistocin ba tare da wata rantsuwa ba,

  13. shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, ba kuwa zai canja zuciyarsa ba, ‘Kai firist ne na har abada.’ ”

  14. Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.

  15. Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama.

  16. Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa.

  17. Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.