Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The High Priest

142 ayoyi · 65 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.

  2. Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.

  3. Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.

  4. Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,

  5. suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”

  6. Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”

  7. Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.

  8. Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’

  9. Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”

  10. Sai waninsu, mai suna Kayifas, wanda ya kasance babban firist a shekarar ya ce, “Ku dai ba ku san kome ba!

  11. Ba ku gane ba, ai, gwamma mutum ɗaya yă mutu saboda mutane da duk ƙasar ta hallaka.”

  12. Bai faɗa haka bisa nufinsa ba, sai dai a matsayinsa na babban firist a shekarar, ya yi annabci ne cewa Yesu zai mutu saboda ƙasar Yahudawa,

  13. ba don ƙasan nan kaɗai ba amma don yă tattaro ’ya’yan Allah da suke warwatse ma, su zama ɗaya.

  14. Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin.

  15. Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce,

  16. “Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.”

  17. Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama.

  18. Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.”

  19. Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu.

  20. Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su.

  21. Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.”

  22. Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.”

  23. Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa.

  24. Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!”

  25. Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”