Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 35:17kusan 1491 K.H.

    Labulen filin tenti da sandunansa da tussansa, da kuma labulen ƙofar shiga fili;

  2. Fitowa 35:18kusan 1491 K.H.

    turakun tenti don tabanakul da kuma don filin, da igiyoyinsu;

  3. Fitowa 35:19kusan 1491 K.H.

    saƙaƙƙun riguna na sawa don hidima cikin wuri mai tsarki da tsarkakakkun riguna na Haruna firist, da riguna don ’ya’yansa maza lokacin da suke aiki a matsayin firistoci.”

  4. Fitowa 35:20kusan 1491 K.H.

    Sai dukan jama’ar Isra’ilawa suka janye daga fuskar Musa,

  5. Fitowa 35:21kusan 1491 K.H.

    duk waɗanda suke da niyya, waɗanda kuma zukatansu suka motsa su, suka kawo kyautai wa Ubangiji, don aikin Tentin Sujada, don duk aikinsa, da don tsarkakakkun riguna.

  6. Fitowa 35:22kusan 1491 K.H.

    Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji.

  7. Fitowa 35:23kusan 1491 K.H.

    Kowane mutumin da yake da shuɗi, shunayya ko jan zare, ko lallausan lilin, ko gashin akuya, ko fatun rago da aka rina ja, ko fatun shanun teku, suka kawo.

  8. Fitowa 35:24kusan 1491 K.H.

    Masu miƙa kyautar azurfa, ko tagulla suka kawo su a matsayin kyautai ga Ubangiji, kuma kowane mutumin da yake da itacen ƙirya don kowane sashin aikin, ya kawo.

  9. Fitowa 35:25kusan 1491 K.H.

    Kowace mace mai fasaha ta kaɗa zare da hannuwanta, ta kuma kawo abin da ta kaɗa na shuɗi, shunayya, ko jan zare, ko lallausan lilin.

  10. Fitowa 35:26kusan 1491 K.H.

    Kuma dukan matan da suke da niyya, suke kuma da fasaha, suka kaɗa gashin akuya.

  11. Fitowa 35:27kusan 1491 K.H.

    Shugabannin suka kawo duwatsun Onis. Da duwatsu masu daraja don a jera a kan efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.

  12. Fitowa 35:28kusan 1491 K.H.

    Suka kawo kayan yaji da man zaitun don fitila da don man shafewa da kuma don turare mai ƙanshi.

  13. Fitowa 35:29kusan 1491 K.H.

    Dukan mazan Isra’ilawa da matan da suke da niyya suka kawo wa Ubangiji kyautai na yardar rai, domin dukan aikin da Ubangiji ya umarce su ta bakin Musa.

  14. Fitowa 35:30kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda,

  15. Fitowa 35:31kusan 1491 K.H.

    ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu,

  16. Fitowa 35:32kusan 1491 K.H.

    don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla.

  17. Fitowa 35:33kusan 1491 K.H.

    Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta.

  18. Fitowa 35:34kusan 1491 K.H.

    Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu.

  19. Fitowa 35:35kusan 1491 K.H.

    Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne.

  20. Fitowa 36:1kusan 1491 K.H.

    Saboda haka Bezalel, Oholiyab da kowane mutumin da Ubangiji ya ba shi basira da iyawa, na sanin yadda za a yi duk aikin shirya wuri mai tsarki, za su yi aiki yadda Ubangiji ya umarta.”

  21. Fitowa 36:2kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Musa ya kira Bezalel da Oholiyab da kowane mutumin da Ubangiji ya ba shi iyawa da kuma wanda ya yi niyya yă yi aiki.

  22. Fitowa 36:3kusan 1491 K.H.

    Suka karɓa daga wurin Musa dukan kyautai da Isra’ilawa suka kawo don su yi aikin shirya wuri mai tsarki. Mutane suka ci gaba da kawo kyautai yardar rai kowace safiya.

  23. Fitowa 36:4kusan 1491 K.H.

    Sai dukan masu fasaha waɗanda suke aikin wuri mai tsarki suka ɗan dakata

  24. Fitowa 36:5kusan 1491 K.H.

    suka ce wa Musa, “Mutane suna kawo fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.”

  25. Fitowa 36:6kusan 1491 K.H.

    Sai Musa ya ba da umarni, suka aika ko’ina a cikin sansani cewa, “Kada namiji ko ta mace yă sāke kawo kyauta don wuri mai tsarki.” Ta haka mutane suka daina kawowa.