- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta waɗannan kalmomi, gama bisa ga kalmomin nan, na yi alkawari da kai da kuma Isra’ila.”
Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.
- Fitowa 34:29kusan 1491 K.H.
Sa’ad da Musa ya sauko daga kan Dutsen Sinai tare da alluna biyu na Alkawari a hannuwansa, bai san cewa fuskarsa tana ƙyalli ba saboda zaman da ya yi a gaban Ubangiji.
- Fitowa 34:30kusan 1491 K.H.
Da Haruna da dukan Isra’ila suka ga Musa, fuskarsa kuma tana ƙyalli, sai suka ji tsoron zuwa kusa da shi.
- Fitowa 34:31kusan 1491 K.H.
Amma Musa ya kira su, sai Haruna da dukan shugabannin jama’ar suka zo wurinsa, ya kuwa yi musu magana.
- Fitowa 34:32kusan 1491 K.H.
Daga baya sai dukan Isra’ilawa suka zo kusa da shi, ya kuma ba su dukan dokokin da Ubangiji ya ba shi a Dutsen Sinai.
- Fitowa 34:33kusan 1491 K.H.
Da Musa ya gama magana da su, sai ya lulluɓe fuskarsa.
- Fitowa 34:34kusan 1491 K.H.
Amma duk sa’ad da ya je gaban Ubangiji don yă yi magana da shi, sai yă tuɓe lulluɓin har sai ya fito. Kuma duk sa’ad da ya fito yă faɗa wa Isra’ilawa abin da aka umarce shi,
- Fitowa 34:35kusan 1491 K.H.
sai su ga fuskarsa tana ƙyalli. Sa’an nan Musa yă sāke lulluɓe fuskarsa, har sai ya shiga don yă yi magana da Ubangiji.
- Fitowa 35:1kusan 1491 K.H.
Musa ya tara dukan jama’ar Isra’ilawa ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku, ku yi.
- Fitowa 35:2kusan 1491 K.H.
Kwana shida za ku yi aiki, amma rana ta bakwai za tă zama rana mai tsarki, Asabbaci ne na hutu ga Ubangiji. Duk wanda ya yi aiki a wannan rana dole a kashe shi.
- Fitowa 35:3kusan 1491 K.H.
Kada ku hura wuta a cikin duk mazauninku a ranar Asabbaci.”
- Fitowa 35:4kusan 1491 K.H.
Musa ya ce wa dukan jama’ar Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.
- Fitowa 35:5kusan 1491 K.H.
Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla;
- Fitowa 35:6kusan 1491 K.H.
shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya;
- Fitowa 35:7kusan 1491 K.H.
fatun rago da aka rina ja, da fatun shanun teku; da itacen ƙirya
- Fitowa 35:8kusan 1491 K.H.
da man zaitun don fitila; da kayan yaji don man shafewa, da kuma turare mai ƙanshi;
- Fitowa 35:9kusan 1491 K.H.
duwatsun onis, da sauran duwatsu masu daraja waɗanda za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
- Fitowa 35:10kusan 1491 K.H.
“Duk waɗanda suke da fasaha a cikinku, su zo su yi dukan abin da Ubangiji ya umarta,
- Fitowa 35:11kusan 1491 K.H.
“wato, aikin tabanakul da tentinsa tare da murfinsa, maɗauransa, katakansa, sandunansa da tussansa;
- Fitowa 35:12kusan 1491 K.H.
akwatin alkawari da sandunansa, murfin kafara da labulen da ya rufe shi;
- Fitowa 35:13kusan 1491 K.H.
tebur da sandunansa, da dukan kayansa da kuma burodin kasancewa;
- Fitowa 35:14kusan 1491 K.H.
wurin ajiye fitila da yake don fitilu da kayayyakinsa, fitilu da mai don fitila;
- Fitowa 35:15kusan 1491 K.H.
bagaden turare da sandunansa, man shafewa da turare mai ƙanshi; da labulen ƙofar shiga tabanakul;
- Fitowa 35:16kusan 1491 K.H.
bagaden hadaya ta ƙonawa da rigarsa ta tagulla da sandunansa da duk kayayyakinsa, daron tagulla da wurin ajiye shi.