Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 36:28kusan 1756 K.H.

    ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.

  2. Farawa 36:29kusan 1756 K.H.

    Waɗannan su ne manyan Horiyawa, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,

  3. Farawa 36:30kusan 1756 K.H.

    Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.

  4. Farawa 36:31kusan 1756 K.H.

    Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,

  5. Farawa 36:32kusan 1756 K.H.

    Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.

  6. Farawa 36:33kusan 1869 K.H.

    Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.

  7. Farawa 36:34kusan 1827 K.H.

    Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.

  8. Farawa 36:35kusan 1785 K.H.

    Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.

  9. Farawa 36:36kusan 1743 K.H.

    Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.

  10. Farawa 36:37kusan 1701 K.H.

    Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ya gāje shi.

  11. Farawa 36:38kusan 1659 K.H.

    Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.

  12. Farawa 36:39kusan 1617 K.H.

    Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.

  13. Farawa 36:40kusan 1617 K.H.

    Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne, Timna, Alwa, Yetet.

  14. Farawa 36:41kusan 1617 K.H.

    Oholibama, Ela, Finon.

  15. Farawa 36:42kusan 1617 K.H.

    Kenaz, Teman, Mibzar.

  16. Farawa 36:43kusan 1617 K.H.

    Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.

  17. Farawa 37:1kusan 1728 K.H.

    Yaƙub ya zauna a ƙasar da mahaifinsa ya zauna, wato, ƙasar Kan’ana.

  18. Farawa 37:2kusan 1728 K.H.

    Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa.

  19. Farawa 37:3kusan 1728 K.H.

    Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau.

  20. Farawa 37:4kusan 1728 K.H.

    Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.

  21. Farawa 37:5kusan 1728 K.H.

    Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.

  22. Farawa 37:6kusan 1728 K.H.

    Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi.

  23. Farawa 37:7kusan 1728 K.H.

    Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”

  24. Farawa 37:8kusan 1728 K.H.

    Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.

  25. Farawa 37:9kusan 1728 K.H.

    Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”