- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1900–1700 BC
Jacob, Joseph & Egypt
Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Farawa 36:3kusan 1796 K.H.
ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot.
- Farawa 36:4kusan 1796 K.H.
Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel.
- Farawa 36:5kusan 1796 K.H.
Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.
- Farawa 36:6kusan 1740 K.H.
Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.
- Farawa 36:7kusan 1740 K.H.
Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu.
- Farawa 36:8kusan 1740 K.H.
Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.
- Farawa 36:9kusan 1740 K.H.
Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.
- Farawa 36:10kusan 1774 K.H.
Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isuwa maza, Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
- Farawa 36:11kusan 1734 K.H.
’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.
- Farawa 36:12kusan 1734 K.H.
Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.
- Farawa 36:13kusan 1734 K.H.
’Ya’yan Reyuwel maza su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
- Farawa 36:14kusan 1712 K.H.
’Ya’yan Oholibama maza ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne, Yewush, Yalam da Kora.
- Farawa 36:15kusan 1712 K.H.
Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa, ’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,
- Farawa 36:16kusan 1712 K.H.
Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.
- Farawa 36:17kusan 1712 K.H.
’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
- Farawa 36:18kusan 1712 K.H.
’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa, Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama ’yar Ana matar Isuwa.
- Farawa 36:19kusan 1712 K.H.
Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.
- Farawa 36:20kusan 1806 K.H.
Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,
- Farawa 36:21kusan 1800 K.H.
Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
- Farawa 36:22kusan 1756 K.H.
’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ’yar’uwar Lotan ce.
- Farawa 36:23kusan 1756 K.H.
’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
- Farawa 36:24kusan 1756 K.H.
’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.
- Farawa 36:25kusan 1756 K.H.
’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama ’yar Ana.
- Farawa 36:26kusan 1756 K.H.
’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
- Farawa 36:27kusan 1756 K.H.
’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan.