Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. A can ya gina bagade, ya kuma kira wurin El Betel, gama a can ne Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake gudu daga ɗan’uwansa.

  2. To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.

  3. Bayan Yaƙub ya komo daga Faddan Aram, sai Allah ya bayyana gare shi, ya kuma albarkace shi.

  4. Allah ya ce masa, “Sunanka Yaƙub ne, amma ba za a ƙara kira ka Yaƙub ba; sunanka zai zama Isra’ila.” Saboda haka ya ba shi suna Isra’ila.

  5. Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka.

  6. Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.”

  7. Sa’an nan Allah ya tashi sama daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi.

  8. Yaƙub kuwa ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi magana da shi, ya zuba hadaya ta sha a kansa; ya kuma zuba mai a kansa.

  9. Yaƙub ya kira inda Allah ya yi magana da shi, Betel.

  10. Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai.

  11. Sa’ad da take cikin zafin haihuwa, sai macen da ta karɓi haihuwar ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”

  12. Farawa 35:18kusan 1729 K.H.

    Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin.

  13. Farawa 35:19kusan 1729 K.H.

    Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem).

  14. Farawa 35:20kusan 1729 K.H.

    Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.

  15. Farawa 35:21kusan 1729 K.H.

    Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder.

  16. Farawa 35:22kusan 1729 K.H.

    Yayinda Isra’ila yana zama a wancan yanki, Ruben ya shiga ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya ji labari. Yaƙub ya haifi ’ya’ya maza goma sha biyu.

  17. Farawa 35:23kusan 1729 K.H.

    ’Ya’yan Liyatu maza, Ruben shi ne ɗan fari na Yaƙub. Sauran su ne, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar da Zebulun.

  18. Farawa 35:24kusan 1729 K.H.

    ’Ya’yan Rahila maza su ne, Yusuf da Benyamin.

  19. Farawa 35:25kusan 1729 K.H.

    ’Ya’yan Bilha maza, mai hidimar Rahila su ne, Dan da Naftali.

  20. Farawa 35:26kusan 1729 K.H.

    ’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne, Gad da Asher. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.

  21. Farawa 35:27kusan 1729 K.H.

    Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna.

  22. Farawa 35:28kusan 1729 K.H.

    Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin,

  23. Farawa 35:29kusan 1716 K.H.

    sa’an nan ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuwa mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa da kyakkyawan tsufa da kuma cikakken shekaru. ’Ya’yansa maza, Isuwa da Yaƙub suka binne shi.

  24. Farawa 36:1kusan 1796 K.H.

    Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).

  25. Farawa 36:2kusan 1796 K.H.

    Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye