Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 33:8kusan 1739 K.H.

    Isuwa ya yi tambaya, “Me kake nufi da dukan abubuwan nan da na sadu da su ana korarsu?” Sai Yaƙub ya ce, “Don in sami tagomashi a idanunka ne, ranka yă daɗe.”

  2. Farawa 33:9kusan 1739 K.H.

    Amma Isuwa ya ce, “Na riga na sami abin da ya ishe ni, ɗan’uwana. Riƙe abin da kake da shi don kanka.”

  3. Farawa 33:10kusan 1739 K.H.

    Sai Yaƙub ya ce, “A’a, ina roƙonka, in na sami tagomashi a idanunka, sai ka karɓi wannan kyautai daga gare ni. Gama ganin fuskarka kamar ganin fuskar Allah ne, yanzu da ka karɓe ni da farin ciki.

  4. Farawa 33:11kusan 1739 K.H.

    Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa.

  5. Farawa 33:12kusan 1739 K.H.

    Sa’an nan Isuwa ya ce, “Bari mu tafi, zan yi maka rakiya.”

  6. Farawa 33:13kusan 1739 K.H.

    Amma Yaƙub ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ka san cewa ’ya’yan ƙanana ne, dole in lura da tumaki da shanun da suke shayar da jariransu. In aka kore su da gaggawa a rana guda kaɗai, dukan dabbobin za su mutu.

  7. Farawa 33:14kusan 1739 K.H.

    Saboda haka bari ranka yă daɗe yă sha gaban bawansa, ni kuma in tafi a hankali bisa ga saurin abin da ake kora a gabana da kuma saurin ’ya’yan, sai na iso wurinka ranka yă daɗe, a Seyir.”

  8. Farawa 33:15kusan 1739 K.H.

    Sai Isuwa ya ce, “To, bari in bar waɗansu mutanena tare da kai.” Yaƙub ya ce, “Amma me ya sa za ka yi haka? Bari dai in sami tagomashi a idanunka ranka yă daɗe.”

  9. Farawa 33:16kusan 1739 K.H.

    Saboda haka a wannan rana Isuwa ya kama hanyar komawa zuwa Seyir.

  10. Farawa 33:17kusan 1739 K.H.

    Yaƙub kuwa, ya tafi Sukkot, inda ya gina wuri domin kansa, ya kuma yi bukkoki domin dabbobinsa. Shi ya sa aka kira wurin Sukkot.

  11. Farawa 33:18kusan 1739 K.H.

    Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni.

  12. Farawa 33:19kusan 1739 K.H.

    Ya sayi fili daga ’ya’yan Hamor maza, mahaifin Shekem inda ya kafa tentinsa, a bakin azurfa ɗari.

  13. Farawa 33:20kusan 1739 K.H.

    A can ya kafa bagade ya kuma kira shi El Elohe Isra’ila.

  14. Farawa 34:1kusan 1732 K.H.

    To, Dina, ’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar.

  15. Farawa 34:2kusan 1732 K.H.

    Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.

  16. Farawa 34:3kusan 1732 K.H.

    Zuciyarsa kuwa ta damu da son Dina ’yar Yaƙub, ya kuwa ƙaunaci yarinyar, ya yi mata magana a hankali.

  17. Farawa 34:4kusan 1732 K.H.

    Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.”

  18. Farawa 34:5kusan 1732 K.H.

    Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa an ɓata ’yarsa Dina, sai ya yi shiru game da batun sai ’ya’yansa maza sun dawo gida, gama ’ya’yansa suna a jeji tare da dabbobinsa suna kiwo.

  19. Farawa 34:6kusan 1732 K.H.

    Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub.

  20. Farawa 34:7kusan 1732 K.H.

    Da ’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da ’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba.

  21. Farawa 34:8kusan 1732 K.H.

    Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan ’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura.

  22. Farawa 34:9kusan 1732 K.H.

    Ku yi auratayya da mu; ku aurar mana da ’ya’yanku mata, ku kuma ku auro ’ya’yanmu mata wa kanku.

  23. Farawa 34:10kusan 1732 K.H.

    Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a, ku kuma sami dukiya.”

  24. Farawa 34:11kusan 1732 K.H.

    Sai Shekem ya ce wa mahaifin Dina da kuma ’yan’uwanta. “Bari in sami tagomashi a idanunku, zan kuwa ba ku duk abin da kuka tambaya.

  25. Farawa 34:12kusan 1732 K.H.

    Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.”