- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1900–1700 BC
Jacob, Joseph & Egypt
Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Farawa 50:12kusan 1689 K.H.
Haka fa ’ya’yan Yaƙub maza suka yi yadda ya umarce su.
- Farawa 50:13kusan 1689 K.H.
Suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan’ana suka kuma binne shi a kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, ya zama makabarta daga Efron mutumin Hitti.
- Farawa 50:14kusan 1689 K.H.
Bayan ya binne mahaifinsa, sai Yusuf ya koma Masar, tare da ’yan’uwansa da kuma dukan waɗanda suka tafi tare da shi don binne mahaifinsa.
- Farawa 50:15kusan 1689 K.H.
Sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka ga cewa mahaifinsu ya mutu, sai suka ce, “Mai yiwuwa Yusuf yana riƙe da mu a zuciya, wataƙila zai rama dukan abubuwa marasa kyau da muka yi masa?”
- Farawa 50:16kusan 1689 K.H.
Saboda haka suka aika wa Yusuf suna cewa, “Mahaifinka ya bar waɗannan umarnai kafin yă rasu.
- Farawa 50:17kusan 1689 K.H.
Ga abin da za ku ce wa Yusuf, ‘Na roƙe ka, ka gafarta wa ’yan’uwanka zunubai da laifofin da suka aikata na abubuwa marasa kyau da suka yi maka.’ Yanzu muna roƙonka ka gafarta zunuban bayin Allah na mahaifinka.” Sa’ad da saƙonsu ya zo masa, sai Yusuf ya yi kuka.
- Farawa 50:18kusan 1689 K.H.
’Yan’uwansa kuwa suka zo suka fāɗi a gabansa suka ce, “Mu bayinka ne.”
- Farawa 50:19kusan 1689 K.H.
Amma Yusuf ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Ni Allah ne?
- Farawa 50:20kusan 1689 K.H.
Kun yi niyya ku yi mini lahani, amma Allah ya nufe wannan ya zama alheri don yă cika abin da yanzu yake faruwa, ceton rayuka masu yawa.
- Farawa 50:21kusan 1689 K.H.
Saboda haka, kada ku ji tsoro. Zan tanada muku da kuma ’ya’yanku.” Ya sāke tabbatar musu, ya kuma yi musu magana ta alheri.
- Farawa 50:22kusan 1689 K.H.
Yusuf ya zauna a Masar tare da dukan iyalin mahaifinsa. Ya rayu shekara ɗari da goma.
- Farawa 50:23kusan 1689 K.H.
Ya kuma ga tsara ta uku ta ’ya’yan Efraim. Haka ma ’ya’yan Makir ɗan Manasse, an haife su aka sa a gwiwoyin Yusuf.
- Farawa 50:24kusan 1689 K.H.
Sai Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa. Amma tabbatacce Allah zai taimake ku, yă fid da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.”
- Farawa 50:25kusan 1689 K.H.
Yusuf kuwa ya sa ’ya’yan Isra’ila maza suka yi rantsuwa, ya kuma ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, ku kuma dole ku ɗauki ƙasusuwana, ku haura da su daga wannan wuri.”
- Farawa 50:26kusan 1689 K.H.
Yusuf kuwa ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Bayan an shafe shi da maganin hana ruɓa, sai aka sa shi a akwatin gawa a Masar.