Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 48:17kusan 1689 K.H.

    Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse.

  2. Farawa 48:18kusan 1689 K.H.

    Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.”

  3. Farawa 48:19kusan 1689 K.H.

    Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.”

  4. Farawa 48:20kusan 1689 K.H.

    Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.

  5. Farawa 48:21kusan 1689 K.H.

    Sa’an nan Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ina gab da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku

  6. Farawa 48:22kusan 1689 K.H.

    Kuma gare ka, a matsayi wanda yake kan ’yan’uwanka, na ba da gonar da na karɓe daga Amoriyawa da takobi da kuma bakana.”

  7. Farawa 49:1kusan 1689 K.H.

    Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.

  8. Farawa 49:2kusan 1689 K.H.

    “Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza; ku saurari mahaifinku, Isra’ila.

  9. Farawa 49:3kusan 1689 K.H.

    “Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko.

  10. Farawa 49:4kusan 1689 K.H.

    Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba, gama ka hau gadon mahaifinka ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.

  11. Farawa 49:5kusan 1689 K.H.

    “Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne, takubansu makamai ne na tā da hankali.

  12. Farawa 49:6kusan 1689 K.H.

    Ba zan shiga shawararsu ba, ba zan shiga taronsu ba, gama sun kashe maza cikin fushinsu cikin ganin dama suka kashe bijimai.

  13. Farawa 49:7kusan 1689 K.H.

    La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila.

  14. Farawa 49:8kusan 1689 K.H.

    “Yahuda, ’yan’uwanka za su yabe ka; hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka, ’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.

  15. Farawa 49:9kusan 1689 K.H.

    Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda, ka dawo daga farauta, ɗana. Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe, kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?

  16. Farawa 49:10kusan 1689 K.H.

    Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba, ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba, sai ya zo ga wanda yake mai shi. Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.

  17. Farawa 49:11kusan 1689 K.H.

    Zai daure jakinsa a kuringa, aholakinsa a rassa mafi kyau; zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.

  18. Farawa 49:12kusan 1689 K.H.

    Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi, haƙorarsa farare kamar madara.

  19. Farawa 49:13kusan 1689 K.H.

    “Zebulun zai zauna a bakin teku, yă zama tasar jiragen ruwa; iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.

  20. Farawa 49:14kusan 1689 K.H.

    “Issakar doki mai ƙarfi, kwance tsakanin buhunan sirdi.

  21. Farawa 49:15kusan 1689 K.H.

    Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau da kuma daɗin da ƙasarsa take, zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi yă miƙa kai ga aikin dole.

  22. Farawa 49:16kusan 1689 K.H.

    “Dan zai tanada adalci wa mutanensa kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.

  23. Farawa 49:17kusan 1689 K.H.

    Dan zai zama maciji a gefen hanya, kububuwa a bakin hanya, da take saran ɗiɗɗigen doki domin mahayinsa yă fāɗi da baya.

  24. Farawa 49:18kusan 1689 K.H.

    “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.

  25. Farawa 49:19kusan 1689 K.H.

    “Masu fashi za su fāɗa wa Gad, amma zai runtume su.