Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sickness

120 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.

  2. Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke.

  3. Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.

  4. Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.

  5. Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukanmu.”

  6. Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.

  7. Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?” Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.”

  8. Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”;

  9. Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

  10. Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu

  11. suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

  12. “Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.

  13. da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’

  14. “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’

  15. da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’

  16. “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’

  17. Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.

  18. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa,

  19. domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.”

  20. Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.

  21. Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?”

  22. Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ ”

  23. Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi.

  24. Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru.

  25. Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”