Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sickness: Often sent as a punishment of sin

8 ayoyi · 47 fannoni

Ayoyi game da Often sent as a punishment of sin

  1. “ ‘Amma in za ku kasa kunne gare ni, ku kuma aikata dukan waɗannan umarnai,

  2. in kuka kuma ƙi farillaina, kuka yi ƙyamar dokokina, kuka kuma kāsa kiyaye umarnaina, har kuka karya alkawarina,

  3. to, zan yi muku wannan. Zan kawo muku abin bantsoro, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idonku, yă kuma sa ranku a wahala. Za ku shuka iri a banza, domin abokan gābanku ne za su ci.

  4. Yehoram ya sami wasiƙa daga Iliya annabi, wadda ta ce, “Ga abin da Ubangiji Allah na kakanka Dawuda ya ce, ‘Ba ka yi tafiya a hanyoyin mahaifinka Yehoshafat ko Asa sarkin Yahuda ba.

  5. Amma ka yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, ka sa Yahuda ya kauce, ka kuma sa mutanen Urushalima suka yi karuwanci, kamar yadda gidan Ahab ta yi. Ka kuma kashe ’yan’uwanka, membobi gidan mahaifinka, mutanen da suka fi ka kirki.

  6. Saboda haka a yanzu Ubangiji yana shirin ya bugi mutanenka, ’ya’yanka maza, matanka da kuma kome da yake naka, da bugu mai ƙarfi.

  7. Kai kuma za ka kamu da ciwon hanji wanda zai yi ta cinka kowace rana sai har hanjinka sun fito.’ ”

  8. Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci.