Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sickness: Through the touch of his garment

10 ayoyi · 47 fannoni

Ayoyi game da Through the touch of his garment

  1. Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu

  2. suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

  3. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa,

  4. domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.”

  5. Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.

  6. Nan da nan Yesu ya gane cewa, iko ya fita daga gare shi. Sai ya juya a cikin taron ya yi tambaya, “Wa ya taɓa rigata?”

  7. Sai almajiransa suka ce, “Kana ganin mutane suna matsinka, duk da haka kana tambaya, ‘Wa ya taɓa ni?’ ”

  8. Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi.

  9. Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru.

  10. Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”