Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sickness: Often manifests saving grace to sinners during

11 ayoyi · 47 fannoni

Ayoyi game da Often manifests saving grace to sinners during

  1. “Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,

  2. yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi.

  3. Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.

  4. Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.

  5. Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi,

  6. yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’

  7. Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.

  8. Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa.

  9. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.

  10. Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari.

  11. Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.