Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sickness: Acknowledge that, comes from God

10 ayoyi · 47 fannoni

Ayoyi game da Acknowledge that, comes from God

  1. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka.

  2. Ka juye kunnenka gare ni, ka zo da sauri ka cece ni; ka zama dutsen mafakata, mafaka mai ƙarfi na cetona.

  3. Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata, saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.

  4. Ka ’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini, gama kai ne mafakata.

  5. Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.

  6. Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza; na dogara ga Ubangiji.

  7. Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikin ƙaunarka, gama ka ga azabata ka kuma san wahalar raina.

  8. Ba ka ba da ni ga abokin gāba ba amma ka sa ƙafafuna a wuri mai sarari.

  9. Kamar tentin makiyayi an rushe gidana aka kuma ƙwace ta daga gare ni. Kamar mai saƙa, na nannaɗe rayuwata, ya kuma yanke ni daga sandar saƙa; dare da rana ka kawo ni ga ƙarshe.

  10. Amma me zan ce? Ya riga ya yi mini magana, shi kansa ne kuma ya aikata. Zan yi tafiya da tawali’u dukan kwanakina saboda wahalar raina.