Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Righteousness

480 ayoyi · 132 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.

  2. A hanyar adalci akwai rai; a wannan hanya akwai rashin mutuwa.

  3. Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi.

  4. Masu adalci sukan ci isashen abinci, amma cikin mugaye na fama da yunwa.

  5. Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane.

  6. Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala.

  7. Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.

  8. Ubangiji yana nesa da mugaye amma yakan ji addu’ar adalai.

  9. Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau, gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne.

  10. Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.

  11. Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.

  12. Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa.

  13. ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci.

  14. Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa, amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki.

  15. Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa, amma mugaye ba su da wannan damuwa.

  16. Ku faɗa wa masu adalci cewa kome zai zama musu da kyau, gama za su ji daɗin aikin da hannuwansu suka yi.

  17. Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.

  18. amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.

  19. Adalci ne zai zama abin ɗamararsa aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.

  20. Raina yana marmarinka da dare; da safe kuma raina yana son ganinka. Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya, mutanen duniya kan koyi adalci.

  21. Ko da yake akan nuna wa mugaye alheri, ba sa koyi adalci; har ma a ƙasar masu aikata gaskiya sukan ci gaba da aikata mugunta ba sa ganin girmar darajar Ubangiji.

  22. Zan mai da gaskiya igiyar gwaji adalci kuma ɗan katakon gwajin ginin; ƙanƙara za tă share mafakarku, ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku.

  23. Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci masu mulki kuma su yi mulki da adalci.

  24. Aikin gaskiya zai zauna a hamada adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi.

  25. Aikin adalci zai zama salama; tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.