Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Righteousness

480 ayoyi · 132 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.

  2. Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki.

  3. Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.

  4. Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne!

  5. Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.

  6. Saboda haka ’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah.

  7. Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa.

  8. Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.

  9. Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.

  10. Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.

  11. Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;

  12. Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya;

  13. amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba.

  14. Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.”

  15. Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah.

  16. Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.

  17. Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”

  18. Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,

  19. duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane.

  20. Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna.

  21. Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba.

  22. Ya kamata kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yă gina shi.

  23. Gama ko Kiristi ma bai gamshi kansa ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zage-zagen da waɗansu suka yi maka, duk sun fāɗo a kaina.”

  24. Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.

  25. Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yă ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu,