Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles Wrought Through Servants of God: Various miracles

6 ayoyi · 74 fannoni

Ayoyi game da Various miracles

  1. Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’

  2. Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”

  3. Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa.

  4. Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa.

  5. Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.

  6. Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki.