Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles Wrought Through Servants of God: Child restored to life

4 ayoyi · 74 fannoni

Ayoyi game da Child restored to life

  1. Da Elisha ya isa gidan, sai ga gawar yaron kwance a kan gadonsa.

  2. Sai ya shiga, ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji.

  3. Sa’an nan ya hau gadon yă kwanta a bisa yaron, ya miƙe a kansa, baki da baki, ido da ido, hannu da hannu. Yayinda ya miƙe kansa a kan yaron, sai jikin yaron ya ɗau ɗumi.

  4. Elisha ya tashi, ya yi ta kai komo a cikin ɗakin. Sa’an nan ya sāke koma kan gadon yă miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa sau bakwai, ya kuma buɗe idanunsa.