Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miracles Wrought Through Servants of God: Waters of Jordan divided

10 ayoyi · 74 fannoni

Ayoyi game da Waters of Jordan divided

  1. Ta haka ne za ku san cewa Allah mai rai yana tare da ku, kuma ba shakka a gabanku za ku gani zai kore Kan’aniyawa, Hittiyawa, Hiwiyawa, Ferizziyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa da Yebusiyawa.

  2. Ku duba, akwatin alkawarin Ubangiji na dukan duniya zai yi gaba cikin Urdun kafin ku.

  3. Yanzu sai ku zaɓi mutum goma sha biyu daga kabilan Isra’ila, ɗaya daga kowace kabila.

  4. Kuma da firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangiji dukan duniya, sun sa ƙafa cikin ruwan kogin Urdun, ruwan da yake gudu a rafin zai tsaya cik yă taru a wuri ɗaya.”

  5. Saboda haka sa’ad da mutanen suka tashi don su ƙetare Urdun, firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka sha gaba.

  6. Da kaka Urdun yakan cika makil da ruwa. Duk da haka da zarar firistoci masu ɗauke da akwatin alkawari suka tsoma ƙafafunsu a gefen ruwa,

  7. sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko.

  8. Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.

  9. Sai Iliya ya tuɓe rigarsa, ya nannaɗe ya bugi ruwan Urdun da shi. Sai ruwan ya dāre gida biyu, suka haye a busasshiyar ƙasa.

  10. Sa’an nan Elisha ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya bugi ruwan da shi. Ya ce, “Yanzu ina Ubangiji Allah na Iliya?” Da ya bugi ruwan sai ruwan ya dāre gida biyu, sai ya haye.