Skip to content

Ashkelon

11 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Askelon

31.6600, 34.5400 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Ashkelon

  1. Mutanen Yahuda kuma suka ci Gaza, Ashkelon, da Ekron, kowace birni tare da yankinsa.

  2. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko masa da iko. Sai ya fita ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutanensu talatin, ya kwashe kayansu ya kuma ba da rigunarsu ga waɗanda suka bayyana kacici-kacicin. Cike da fushi, ya haura zuwa gidan mahaifinsa.

  3. Waɗannan su ne siffofi marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin miƙa hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.

  4. “Kada a faɗe shi a Gat, kada a yi shelarsa a titunan Ashkelon, don kada ’yan matan Filistiyawa su yi murna don kada ’yan matan marasa kaciya su yi farin ciki.

  5. da dukan baƙin da suke can; dukan sarakunan Uz; dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod);

  6. Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki; Ashkelon zai yi shiru. Ya raguwar da suke zama a fili, har yaushe za ku tsattsage kanku?

  7. Amma ta yaya zai huta sa’ad da Ubangiji ya umarta, sa’ad da ya umarta shi don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”

  8. Zan hallaka sarkin Ashdod da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon. Zan hukunta Ekron, har sai dukan Filistiyawa sun mutu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  9. Za a yashe Gaza a kuma bar Ashkelon kango. Da tsakar rana Ashdod za tă zama babu kowa a kuma tumɓuke Ekron.

  10. Za tă zama mallakar raguwar gidan Yahuda; a can za su sami wurin kiwo. Da yamma za su kwanta a gidajen Ashkelon. Ubangiji Allahnsu zai lura da su; zai maido musu da martabarsu.

  11. Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro; Gaza za tă yi birgima cikin azaba, haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya. Gaza za tă rasa sarkinta za a kuma gudu a bar Ashkelon.