Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake mugaye a inda ka tsaya.

  2. Ka bizne su duka tare ka rufe fuskokinsu a cikin kabari.

  3. Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa hannun damanka zai iya cetonka.

  4. “Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa.

  5. Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta ikonta yana cikin tsokar cikinta.

  6. Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul; jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.

  7. Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe.

  8. Tana ta farko cikin ayyukan Allah, Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi.

  9. Tuddai su suke tanada mata abinci a inda duk namun jeji suke wasa.

  10. Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus ta ɓuya cikin kyauro da fadama.

  11. Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji, itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.

  12. Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba; ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.

  13. Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo, ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta?

  14. “Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi ko kuma ka daure harshenta da igiya?

  15. Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?

  16. Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai? Ko za tă yi maka magana a hankali?

  17. Za tă yi yarjejjeniya da kai don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta?

  18. Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu? Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata?

  19. ’Yan kasuwa za su saye ta ko za su raba ta a tsakaninsu?

  20. Ko za ka iya huda fatarta da kibiya ka kuma huda kansa da māsu?

  21. In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba!

  22. Duk ƙoƙarin kama ta banza ne; ganin ta kawai abin tsoro ne.

  23. Ba wanda ya isa yă tsokane ta. Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni?

  24. Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne.

  25. “Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba.