Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God: Faithfulness of

75 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Faithfulness of

Tace bisa littafi
  1. zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba.

  2. Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.”

  3. Na kuma kafa alkawari da su don in ba su ƙasar Kan’ana, inda suka yi zaman baƙunci.

  4. Ban da haka ma, na ji nishe-nishen Isra’ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuma tuna da alkawarina.

  5. Duk da haka, sa’ad da suke a ƙasar abokan gābansu, ba zan ƙi su, ko in yi ƙyamarsu, in hallaka su ƙaƙaf, har in karya alkawarina da su ba. Ni ne Ubangiji Allahnsu.

  6. Amma saboda su, zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu, waɗanda na fitar da su daga Masar a idon al’ummai, don in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.’ ”

  7. Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar.

  8. Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa.

  9. Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata.

  10. Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka.

  11. ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu.

  12. Ka kiyaye alkawarinka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina. Da bakinka ka yi alkawari, da hannunka kuma ka cika shi, yadda yake a yau.

  13. Sa’an nan ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannuwansa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce,

  14. ‘Tun ranar na da fitar da mutanena daga Masar, ban zaɓi wani birni a wata kabilar Isra’ila don a gina haikali domin Sunana ya kasance a can ba, ba kuwa zaɓi wani yă zama shugaba a bisa jama’ata Isra’ila ba.

  15. Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’

  16. “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a zuciyarsa yă gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  17. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Domin yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka kasance da wannan a zuciyarka.

  18. Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikalin, amma ɗanka wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’

  19. “Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina yanzu kuwa na zauna a kan kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  20. A can na ajiye akwatin alkawari, inda alkawarin Ubangiji da ya yi da mutanen Isra’ila yake.”

  21. Sa’an nan Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa sama.

  22. Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama.

  23. Ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama da kuma ƙasa, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna tare da bayinka waɗanda suke cin gaba da zuciya ɗaya a hanyarka.

  24. Ka kiyaye alkawarinka ga bawanka Dawuda mahaifina; da bakinka ka yi alkawari kuma da hannunka ka cika shi, yadda yake a yau.

  25. “Kai ne Ubangiji Allah, wanda ya zaɓi Abram, ya fitar da shi daga Ur na Kaldiyawa, ya kuma ba shi suna Ibrahim.