Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God: Omniscient
Ayoyi game da Omniscient
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni.
Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa.
Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina.
Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.
Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina.
Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane.