Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God: Unclassified scriptures relating to

354 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Unclassified scriptures relating to

Tace bisa littafi
  1. “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata.

  2. Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa.

  3. Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki.

  4. Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki.

  5. Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.

  6. Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.

  7. Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke.

  8. Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.

  9. Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru.

  10. “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.

  11. Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.

  12. Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka.

  13. Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.

  14. “Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?

  15. Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.

  16. Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?

  17. Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa.

  18. Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta.

  19. Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske.

  20. Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.

  21. Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.

  22. Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.

  23. Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.

  24. Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’

  25. Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.