Skip to content

Hermon

7 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Hermonites

33.4100, 35.8500 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Hermon

  1. (Hermon ne Sidoniyawa suke kira Siriyon, Amoriyawa kuwa suna kira shi Senir.)

  2. Wannan ƙasa ta tashi daga Arower a kewayen Kwarin Arnon zuwa Dutsen Siyon (wato, Hermon),

  3. ya kuma aika zuwa ga Kan’aniyawa a gabas da yamma; da kuma zuwa ga Amoriyawa, Hittiyawa da Ferizziyawa, da Yebusiyawa da suke kan tuddai; da kuma Hiwiyawa masu zama a gindin dutsen Hermon a yankin Mizfa.

  4. Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.

  5. Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.

  6. Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.

  7. Ki tare da ni daga Lebanon, amaryata, zo tare da ni daga Lebanon. Ki gangara daga ƙwanƙolin Amana, daga ƙwanƙolin Senir, ƙwanƙolin Hermon, daga ramin zaki da kuma dutsen da damisoshi suke zama.