Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana zan tambaye ka, kuma za ka amsa mini.’

  2. Kunnuwana sun ji game da kai amma yanzu na gan ka.

  3. Saboda haka na rena kaina na kuma tuba cikin ƙura da toka.”

  4. Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,

  5. wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?

  6. Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.

  7. Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,

  8. Zabura ta Dawuda. Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;

  9. gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.

  10. Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.

  11. Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.

  12. Yini naka ne, dare kuma naka ne; ka kafa rana da wata.

  13. Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya; ka yi rani da damina.

  14. Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.

  15. Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.

  16. Maskil na Etan dangin Ezra. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai.

  17. Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta.

  18. Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.

  19. Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.

  20. amma ba zan ɗauke ƙaunata daga gare shi ba, ba kuwa zan taɓa rasa cika amincina ba.

  21. Ba zan take alkawarina ba ko in canja abin da leɓunana suka ambata.

  22. Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci. Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,

  23. don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,

  24. Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,

  25. suna shela cewa, “Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”