Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

  2. Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

  3. Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka.

  4. Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti

  5. ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye. Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa yana hawa a kan fikafikan iska.

  6. Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa.

  7. Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.

  8. Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.

  9. Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;

  10. suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.

  11. Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba.

  12. Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka; yana gudu tsakanin duwatsu.

  13. Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji; jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.

  14. Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan; suna rera cikin rassa.

  15. Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama; ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.

  16. Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu, tsire-tsire domin mutum ya nome, suna fid da abinci daga ƙasa,

  17. ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna, mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske, abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.

  18. Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai, al’ul na Lebanon da ya shuka.

  19. A can tsuntsaye suke sheƙunnansu; shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir.

  20. Manyan duwatsu na awakin jeji ne; tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.

  21. Wata ne ke ƙididdigar lokuta, rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.

  22. Ka yi duhu, sai ya zama dare, sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.

  23. Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta suna kuma neman abincinsu daga Allah.

  24. Rana ta fito, sai suka koma shiru; suka koma suka kwanta a kogwanninsu.

  25. Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma.