Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  2. Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  3. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni.

  5. Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa.

  6. Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina.

  7. Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.

  8. Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina.

  9. Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane.

  10. Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.

  11. Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.

  12. Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri.

  13. Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka.

  14. Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?

  15. Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.

  16. Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

  17. Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.

  18. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.

  19. Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.

  20. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,

  21. da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,

  22. Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

  23. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  24. kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya.

  25. Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,