Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka.

  2. Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami.

  3. A can jiragen ruwa suna kai komo, kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.

  4. Waɗannan duka suna dogara gare ka don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.

  5. Sa’ad da ba su da shi, sai su tattara shi; sa’ad da ka buɗe hannunka, sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.

  6. Sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai su razana; sa’ad da ka ɗauke numfashinsu, sai su mutu su kuma koma ga ƙura.

  7. Sa’ad da ka aika da Ruhunka, sai su halittu, su kuma sabunta fuskar duniya.

  8. Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada; bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa,

  9. shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.

  10. Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.

  11. Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.

  12. Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama.

  13. Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.

  14. Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne.

  15. Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.

  16. Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa.

  17. Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai.

  18. Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama.

  19. Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima.

  20. Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

  21. tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.

  22. Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.

  23. Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya; yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.

  24. Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  25. Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce.