- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Korintiyawa 15:38kusan 59 M.
Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta.
- 1 Korintiyawa 15:39kusan 59 M.
Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu.
- 1 Korintiyawa 15:40kusan 59 M.
Akwai jikuna iri na samaniya, akwai kuma jikuna iri na duniya; sai dai darajar jikunan samaniya dabam take, darajar jikunan duniya kuma dabam take.
- 1 Korintiyawa 15:41kusan 59 M.
Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja.
- 1 Korintiyawa 15:42kusan 59 M.
Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka tā da shi kuma ba ya ruɓewa;
- 1 Korintiyawa 15:43kusan 59 M.
akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma tā da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma tā da shi da ƙarfi;
- 1 Korintiyawa 15:44kusan 59 M.
akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya. In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma.
- 1 Korintiyawa 15:45kusan 59 M.
Haka yake a rubuce cewa, “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai.
- 1 Korintiyawa 15:46kusan 59 M.
Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya.
- 1 Korintiyawa 15:47kusan 59 M.
Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito.
- 1 Korintiyawa 15:48kusan 59 M.
Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama.
- 1 Korintiyawa 15:49kusan 59 M.
Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama.
- 1 Korintiyawa 15:50kusan 59 M.
Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba.
- 1 Korintiyawa 15:51kusan 59 M.
Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu
- 1 Korintiyawa 15:52kusan 59 M.
farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu.
- 1 Korintiyawa 15:53kusan 59 M.
Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan.
- 1 Korintiyawa 15:54kusan 59 M.
Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”
- 1 Korintiyawa 15:55kusan 59 M.
“Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?”
- 1 Korintiyawa 15:56kusan 59 M.
Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko.
- 1 Korintiyawa 15:57kusan 59 M.
Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
- 1 Korintiyawa 15:58kusan 59 M.
Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
- 1 Korintiyawa 16:1kusan 59 M.
To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa.
- 1 Korintiyawa 16:2kusan 59 M.
A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.
- 1 Korintiyawa 16:3kusan 59 M.
In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.
- 1 Korintiyawa 16:4kusan 59 M.
In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.